Gwamnan Jigawa Ya Jajanta Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Spread the love

Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi ya jajanta wa al’ummar jihar, waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa.

Aƙalla ƙananan hukumomin jihar 13 ne suka fuskanci ambaliyar, wadda ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Yayin da yake jawabi a wajen rabon tallafin abinci ga mabuƙata, da gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar gwmanatin jihar suka samar, Gwamna Namdi ya ce gwamnatin jihar da ta tarayya na ƙoƙari don tallafa wa mutanen da ambaliyar ta shafa.

Mutum 25 ne dai suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a faɗin jihar, kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, SEMA, Dakta Kabiru Mairiga, ya shaida wa BBC.

Gwamna Namadi ya kuma iyalan mutanen da suka mutu sakamkon iftila’in, da sauran mutanen da suka rasa dukiyoyi da gidajensu, tare da addu’ar Allah ya mayar da alƙairi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *