Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamashinansa na ayyuka na musamman Auwalu Dalladi Sankara.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Jigawa ya fitar, Ismaila Ibrahim Dutse ya ce Gwamna Umar Namadi ya janye dakatarwar ce nan take.
“Idan ba a manta ba, an dakatar da kwamashinan nan ne saboda zarginsa da ake yi da hannu a wani lamari da aka kai ƙara hukumar Hisba ta jihar Kano, kamar yadda Sakataren Gwamnati Bala Ibrahim bayyana,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya ɗauki matakin ne wata kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta wanke shi daga zargin.
Bayanai sun nuna cewa mijin matar da ake zargin kwamashinan ya yi mu’amala da ita ne ya kai ƙara kotun bayan Hisba ta gaza sasanta batun.