Gwamnan jahar Kaduna, Uba Sani , ya dakatar da kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan daga mukaminsa tare da maye gurbinsa da James Atung Kanyip.
Sanarwar hakan Mai dauke da sa Hannun babban sakataren yada Labaran Gwamnan, Ibrahim Musa.
Haka zalika Gwamnan ya nada Ibrahim Tanko Muhammed, a matsayin kwamishinan kudi, Barde Yunana Markus kwamishinan ma’aikatar Jin Kai da kuma Farida Abubakar Ahmed a matsayin daraktan hukumar gidan radiyon Kaduna (KSMC).
Wadannan nade-nade na da daga cikin sauye-sauyen da Gwamnan ya Yi , ciki harda nada wasu masu bashi shawara.
- Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Zargin Biyan Yan Bindiga Kudi Don Yin Sulhu
- Saudiyya na dab da samun damar karɓar baƙuncin gasar cin Kofin Duniya na 2034