Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Sauke Shugabannin Riko 44 Nan Ta Ke

Spread the love

Gwannan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke dukkanin shugabanin riko na kananan hukumomin jihar 44 nan take.

Gwamnan ya bada umarnin ne yayin taro na musamman da ya yi da shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Kano 44 a gidan gwamnati.

Ya umarci shugabannin rikon da su mika jagorancin kananan hukumomin zuwa daraktocin mulki na kowace karamar hukuma.

Ya Kara da cewa, umarnin saukewar ya hada da mataimakan shugabanni da sakatarori da kansiloli na kowace karamar hukuma.

Ya gode musu bisa gudummawar da suka bayar wajen cigaban yankunansu tare da jaddada cewa gwamnati zata ci gaba da tafiya dasu a guraben da suka dace.

A nasu bangaren, shugabannin rikon sun godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya basu na hidimtawa al’umarsu tsawon wannan lokaci.

Radio Kano Facebook.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *