Gwamnan Kano Abba ya haramta ‘duk wani nau’i na zanga-zanga’

Spread the love

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta gudanar “duk wani nau’in taro da zimmar zanga-zanga” a faɗin jihar yayin da ake ci gaba da tirka-tirka tsakanin sarakunan Kano biyu.

Gwamnan ya yi iƙirarin cewa ‘yan jam’iyyar adawa na yunƙurin ɗaukar nauyin wasu ɗalibai daga wasu jihohi don tayar da hankali a jihar, kamar yadda mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Laraba.

“Gwamnan ya bai wa ‘yansanda, da ‘yansandan farin kaya, da jami’an tsaron Civil Defence umarnin kamawa da tsarewa da tuhumar duk wani mutum ko ƙungiya da suka shiga zanga-zanga a kan titunn Kano,” in ji sanarwar.

Duk da cewa ana ci gaba da zama lafiya da kuma harkoki kamar yadda aka saba a birnin, kawunan Kanawan sun rarrabu game da sarkin da ke mulkin masarautar jihar tsakanin Muhammadu Sanusi II da kuma Aminu Ado Bayero.

Yanzu haka kowannensu na da umarnin kotu biyu-biyu da ke hana jami’an tsaro fitar da shi daga fada ko kuma sauke shi a matsayin sarkin Kano, Sanusi na zaman fada a fadar Gidan Dabo, yayin da Aminu ke nasa zaman a gidan sarki na Nassarawa.

A cewar Sanusi Bature, Gwamna Abba Kabir ya ce: “Mun samu bayanan sirri cewa wasu manyan ‘yan jam’iyyar adawa na shirin ɗaukar nauyin ɗalibai da ‘yansiyasa daga wasu jihohin arewa maso yamma don haddasa fitina ta hanyar fakewa da zanga-zangar goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero.

“Gwamnatin jiha ta haramta zanga-zanga, da kowane irin maci, sannan duk mutumin da aka gani yana aikata hakan za a kama shi nan take.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *