Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar da za ta samar da masarautu uku masu daraja ta biyu.
Gwamnan ya amince da dokar ne bayan amincewar majalisar dokokin jihar ta Kano a ranar Talata.
Sabuwar dokar ta masarautar Kano da ta ƙunshi sarki mai daraja ta ɗaya guda ɗaya da masu daraja ta biyu guda uku.
Wannan na zuwa bayan hukuncin wata babbar kotun jihar da ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da dokar masarautun Kano ta 2020 ta kafa da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne – waɗanda gwamnatin ta Kano za ta naɗa sarakuna masu daraja ta biyu.