Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Hajiya Hauwa Ibrahim, a matsayin mai riƙon shugabancin tashar talabijin ta jihar, ART ( Abubakar Rimi Television).
Naɗin ya biyo bayan dakatar da Mustapha Indabawa a matsayin manajan darekta na tashar.
A yau Litinin ne Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi, ya fitar da takardar naɗin, inda a cikin wasiƙar ya umarci Hajiya Hauwa Ibrahim ta karɓi ragamar jagorancin tashar, nan take.
Kafin naɗin na yanzu Hajiya Hauwa, ita ce mataimakiyar manajan darektan tashar talabijin ɗin.
Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta Kano ta shigar da tuhuma bakwai a gaban hukumar yaƙi da rashawa ta jihar, kan shugaban da aka dakatar, da kuma babban jami’in ma’aikata na tashar Ibrahim M. Bello – tuhumar da ta ƙunshi aikata mugun laifi da ɓarna da kuma karkatar da kuɗaɗe.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan ƙorafin da aka rubuta wa gwamnan jihar a kan manajan darektan tashar talabijin ɗin.