Gwamnan Kano Ya Jagoranci Sulhunta Baffa Bichi Da Kuma Hamza Maifata

Spread the love

Gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sulhunta sabanin dake Tsakanin sakataren Gwamnatin jahar Dr. Abdullahi Baffa Bichi da kuma Dan takarar shugaban karamar hukumar Bichi a jam’iyar NNPP, Hon. Hamza Maifata Bichi.

Daraktan yada Labaran Gwamnatin jahar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook.

Ya ce shugaban majalissar dokokin jahar Kano, Rt. Hon. Jibrin Isma’il Falgoro, ne ya jagoranci sauran jagororin majalissar zuwa fadar Gwamnatin Kano.

Bature , ya tabbatar da cewa an samu fahimta kuma komai ya koma daidai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *