Gwamnan Kano Ya Kai Ziyarar Duba Mutanen Da Aka Banka Wa Wuta Kano

Spread the love

Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin daukar matakin Shari’a, kan matashin nan mai suna Shafi’u Abubakar, da ake zargi da bankawa jama’a wuta a lokacin da suke yin sallar Asuba, a yankin Unguwar Gadan dake Karamar hukumar Gezawa Kano, inda mutane 24 Suka kone sakamakon Iftila’in.

Gwamnan Abba Kabir, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano, don duba wadanda Suka gamu da iftila’in konewar.

Gwamnan ya yi Allah Wadai da yadda matashin ya Rufe jama’a suna yin sallah, sannan ya banka mu su wuta, inda ya tabbatar da gwamnati ba za ta kyale lamarin ba.

” Wannan hauka ne na karshe, rashin imani ne na karshe , a matsayin mu na wadanda Allah ya dorawa nauyi na tabbatar da kare rayukan Mutane da dukiyoyin al’umma ba za mu bar wannan Abu ba” Abba Kabir Yusuf “.

Abba Kabir Yusuf, ya nesanta batun da siyasa kamar yadda wasu ke fada , harma ya bayyana cewa rigimar cikin gida ce ta rabon gado, sakamakon wani bai ji dadi ba, ya yanke wa kansa hukunci irin na marasa imani.

” Don in banda Kafiri , Wanda Allah ya tsinewa albarka babu Wanda zai zo ya yi wannan ta’addanci shi akansa ya kone bayin Allah”.

Haka zalika gwamnatin jahar Kano, ta yi alkawarin daukar nauyin jinyar wadanda Suka gamu da iftila’in kunar wutar Fetur din.

Idan ba a manta ba jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa , rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta cafke matashin da ake zargi, don fadada Bincike akansa Kafin a Gurfanar da shi a gaban kotu.

A Ranar Lahadin da ta gabata rundunar Yan Sandan jahar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane 17 cikin 24 da Suka ga mu da iftila’in Kunar wutar.

Tawagar gwamnan Kanon da suka ziyarci majinyatan ajiya Lahadi , sun da Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, da kuma Darektan hukumar tsaron farin kaya DSS reshen jahar Kano, da kuma sauran mukarraban gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *