Gwamnan Kano ya saka dokar hana fita a jihar

Spread the love

Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da kafa dokar hana fita a faɗin jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Gwamnan ya kuma umarci jami’an tsaro su tabbatar kowa ya bi wannan doka, wadda aka kafa bayan wasu ɓata-gari sun koma fasa shaguna da gine-gine yayin zanga-zangar matsin rayuwa da ke gudana a faɗin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *