Gwamnan Kano ya yi watsi da yadda tsarin raba abincin azumi a jihar

Spread the love

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan yadda ake gudanar da aikin shirin raba abincin azumi da ake yi a jihar.

Yayin wata ziyarar bazata da ya kai ɗaya daga cibiyoyin da ake aikin raba abincin a Ƙaramar Hukumar Municipal, gwamnan ya nuna rashin jin dadi game da irin abincin da ya gani ana rabawa a cibiyar.

Alala ce da farar shinkafa da manja, inda ya rika tambayar yaran da aka rabawa cewa “manja suke samu ku ba miya ba?”.

Gwamnan ya koka kan yawa da kuma ingancin abinci da ya ga ana rabawa, wanda a cewarsa ya sha banban da abin da gwamnainsa ta amince ta kuma sahale a rika rabawa.

“Wannan wane irin shirme ne,” in ji gwamnan lokacin da yake zantawa da masu dafa abincin, yana tambayarsu wanene ya ba su damar dafa abincin a wannan tsari.

Abba ya ja kunnan masu dafawar tare da ba su sako su shaidawa waɗanda suka ba su damar aikin, cewa kada ya sake dawowa ya tarar da irin wannan abincin da hankalinsa bai kwanta da shi ba.

Najeriya Ta Doke Ghana A Wasan Sada Zumunta

Ɗalibai Tsangaya 15 da aka sace a Jihar Sakoto sun shaki iskar yanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *