Gwamnan jihar Legas babban birnin kasuwancin Najeriya ya yi wa matasa masu yi wa ƙasa hidima na NYSC kyautar naira 100,000 kowannensu da ke cikin rukuni na Stream I ajin Batch B.
Da yake jawabi sanye da kakin hidimar ƙasa yayin bikin sallamar matasan a sansanin horarwa da ke yankin lyana Ipaja, Sanwo Olu ya kuma yi alƙawarin ɗaukar mutum 100 daga cikinsu aiki a jihar.
“Saboda yadda kuka jajirce, kowannenku zai koma gida da N100,000,” in ji shi. “Za a tura muku kuɗin a asusunku mako mai zuwa.”
Kazalika, gwamnan ya yi alƙawarin ware naira biliyan biyar wajen gina sabon sansanin horar da matasan NYSC.
Mutum 4,254 hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta tura jihar Legas domin gudanar da aikin a wannan karon, wanda ake gudanarwa duk shekara bayan mutum ya kammala digiri ko babbar difiloma na farko matuƙar bai wuce shekara 30 ba.