Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, zai fara hutun jinya a yau Laraba, kamar yadda me magana da yawunsa, Richard Olatunde, ya bayyana.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Olatunde ya ce yayin da Akeredolu ke hutun, mataimakin gwamnan, Lucky Aiyedatiwa, zai dauki tafiyar da lamurran jihar, a matsayin mukaddashinsa.
Akeredolu, Babban Lauyan Najeriya (SAN), kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), ya sake lashe zabensa a matsayin gwamnan jihar a watan Oktoban 2020 kuma an rantsar da shi a karo na biyu a watan Fabrairun 2021.
Sai dai kuma, wa’adi na biyu na gwamnan, tun daga watan Janairun 2023, bai kasance cikin kwanciyar hankali ba, domin sai da aka kai shi ƙasar waje neman magani a watan Yuni.
Dan siyasar mai shekaru 67 ya dawo Najeriya ne a watan Satumba bayan watanni da ya yi a ketare, inda ya ci gaba da zama a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Akeredolu dai na fuskantar matsin lamba daga jam’iyyun adawa kan ya yi murabus ko kuma ya miƙa mulki ga mataimakinsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999 ya tanada.
Haka kuma, masu biyayya ga gwamnan a majalisar dokokin jihar sun riƙa yin takun-saka da mataimakin gwamnan, lamarin da ya kai ga har sai da shugaba Bola Tinubu ya sanya baki.
A cikin sanarwarsa, Olatunde ya ce gwamnan zai bayar da fifiko ga lafiyarsa tare da tabbatar da samun cikakkiyar lafiya kafin ya ci gaba da aikinsa.
“Za a aika da wata takarda a hukumance ɗauke da bayani game da hutun jinyar da gwamnan zai yi da kuma sanarwar mika mulki ga mataimakin gwamnan ga majalisar dokokin jihar, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.” In ji sanarwar.
Tun da farko dai, rahotanni a Najeriya sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci majalisar dokokin jihar Ondo ta tabbatar da miƙa harkokin mulki ga matamakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ba tare da wani sharaɗi ba.