Gwamnati Da NLC Za Su Sake Zama Kan Mafi Karancin Albashi.

Spread the love
NLC
NLC

Kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi a ƙasar zai sake zama a mako mai zuwa domin ci gaba da tattauna batun mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙasar, bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar NLC da TUC suka fice daga tattaunawar ranar Larabar da ta gabata 15 ga watan Mayu.

Cikin wasiƙar gayyatar da shugaban kwamitin, Bukar Goni, ya aike wa mambobin kwamitin a matakan jihohi ya ce kwamitin ya amince da sauya matsayarsa kan naira 48,000 da ya ɗauka ranar Larabar.

Wasiƙar ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar, da su gayyaci mambobinsu domin halartar zaman da za a yi ranar Talata 21 ga watan Mayu.

Tun da farko dai ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, lamarin da ya sa tunaninsu da na kwamitin ya yi hannun riga.

A nasu ɓangare, kamfanoni masu zaman kansu sun amince naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun ce sun fice daga tattaunawar ta ranar Laraba ne saboda sun fahimci cewa gwamnatin ƙasar ba da gaske ta yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *