Gwamnati na ƙoƙarin ƙara yawan jami’an tsaro a Najeriya – Sanata Ƴar’adua

Spread the love

Sanata Abdulaziz Yar’adua ya ce gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki domin kara yawan jami’an tsaro domin ƙara murƙushe ayyukan miyagu da ke ƙaruwa a ƙasar.

Najeriya dai na fama da ayyukan ƴanbindiga da sace-sacen jama’a da kuma satar mai da sauran laifuka.

Sanata Yar’adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya ya koka kan adadin jami’an tsaron da ke Najeriya wanda a jumulla ba su kai ko miliyan ɗaya ba a ƙasar da ke da yawan mutum miliyan 220.

Ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels inda ya ce gwamnati tana ƙoƙari domin gyara hakan.

Najeriya da wasu kasashen Afirka sun fuskanci matsalar katsewar internet

Sojoji sun kashe ƴan bindiga a jihar Taraba

Sanata Yar’adua wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji ya ce “dole mu gane cewa muna da matsala da ƙarfin yansanda da sojoji da sauran jami’an tsaron da muke da su.”

A cewarsa, baya ga rashin isassun jami’an tsaro, rashin ci gaba shi me wani abu ne da ke janyo ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *