Gwamnati ta gargaɗi ‘yan Najeriya kan shan gishiri fiye da ƙima

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta ja hankalin ‘yan ƙasar da su rage yawan shan gishiri a abincinsu na yau da kullum domin kariya daga cutuka da ke saurin kisa.

Ministan lafiyar ƙasar, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya yi gargaɗin a ranar Talata lokacin bikin makon taƙayta shan gishiri a Abuja.

Ministan ya ce “shan gishiri fiye da ƙima gishiri na da illa a rayuwarmu inda yake ta’azzara cutar hawan jini wadda ke haddasa bugun zuciya da shanyewar ɓrin jiki”.

Ya ƙara da cewa shan gishiri fiye da ƙima a Najeriya babban abu ne da ke taimakawa da kaso 10 na mace-macen da ake yi a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *