Gwamnati ta rufe katafaren shagon Sahad stores a Abuja

Spread the love

Awa 24 bayan shugaban Nigeria, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hanyoyin dakile matsalar karancin abinci da tsadarsa a kasar, jami’an hukumar da ke kare muradan masu saye ta kasa sun rufe, babban shagon nan na Sahad Stores da ke yankin Area 11 a Abuja.

An dai zargin cewa masu katafaren shagon da kara wa abokan huldarsu kudin kaya fiye da farashin da ke makale a jikin kayan.

Da yake yi wa ‘yan jarida bayani, shugaban hukumar mai kare muradan masu saye ta kasa, Adamu Ahmed Abdullahi ya ce wani bincike da hukumar ta gudanar kan katafaren shagon ya nuna musu yadda masu gudanar wa shagon suke “cutar” masu saye.

Kungiyar ma su motocin sufuri ta kasa RTEAN ta dakatar da shugaban tashar kwanar Dawaki

Tinubu na duba yiwuwar kafa ‘yan sandan jihohi

Ya kara da cewa shagon zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

“ Mun fahimci cewa mutanen nan abun da suke yi yaudara ne inda babu gaskiya da yin abu a faifai dangane da farashin kayan da suke da su wanda kuma hakan ya yi karo da sashe na (135) da dokar da ta hana a yaudari abokin hulda ta hanyar cea ka da mai saye ya biya kudin kaya fiye da abin da ke rubuce a kan kayan.” In ji Adamu Ahmed Abdullahi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *