Gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar kula da ma’adanai ta tabbatar da ayyukan dakarun tsaro 2,220 a karkashin sabon tsarin tsaro, inda ta kuma umarce su da su yi maganin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Haka kuma ta buƙaci sabbin dakarun da su dakile sata da duk wasu munanan ayyuka da suka shafi ma’adinan kasar domin bai wa al’umma damar cin gajiyar amfani da abubuwan da Allah ya hore musu.
Ministan ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayar da wannan umarni a lokacin taron karɓar jami’an da aka horar na musamman da kuma aka zayyana zu daga hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya mai suna “Mining Marshal Corps” a hedikwatar ma’aikatar a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.
Wannan sabon al’amari ya zo ne watanni biyu bayan da Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin ma’aikatu karkashin jagorancin ministan ma’adinai na kasa don yin shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen cimma wa’adinsa na samar da wani tsari na tabbatar da albarkatun kasa da suka hada da ma’adanai da dazuka da kuma tattalin arzikin ruwa.
A cewarsa, kafa dakarun a hukumance zai tabbatar da tsaro a wuraren da ake haƙar ma’adanai, da kawar da baragurbi, da tsaftace muhallin da ake haƙar ma’adanan a cikinsa da kuma safarar ma’adanai daga Najeriya.
Ya bayyana hakan a matsayin babban nasara a cikin ajandarsa guda bakwai.
Ministan ya kara da cewa jami’an hako ma’adinai da aka kirkira domin su zama jami’an tsaro a tsakanin hukumomin za su hada da jami’ai na musamman daga sauran hukumomin tsaro kamar ‘yan sandan Najeriya da sojoji da sauransu.
Da yake jawabi a yayin taron, Alake ya ce, “Rashin tsaro ya durkusar da bangaren tattalin arziƙin ma’adinai tare da hadewa da sauran abubuwan da za su iya haifar da karancin kudaden shiga na ƙasar. Don haka, yaƙi da rashin tsaro a wannan fanni yana da matukar muhimmanci idan za mu sami nasarar cimma wata nasara.”
Ka da wata masarauta ta ɓoye makasan sojoji 17 – Gwamnan Delta
‘Ba za mu bar Okuama ba har sai an zaƙulo waɗanda suka kashe sojojinmu 17’
“Muna fata kuma mun yi imanin cewa ma’adinan za su zama hanyar ceton tattalin arzikin Najeriya.”
A nasa jawabin, kwamandan hukumar rundunar farin kaya ta NSCDC, Abubakar Audi, ya bayyana cewa sabbin jami’an hako ma’adanai za su bai wa hukumar hadin kai wajen kare kadarori da ababen more rayuwa na kasa da ma’adanai.
Audi ya bayyana cewa jami’an tsaron za su yi hulda da hukumar kula da ma’adanai a jihohi domin samun bayanan sirri kuma za su kasance a karkashin jagorancin ministan ma’adanai kai tsaye domin gudanar da aiki yadda ya kamata.