Gwamnati ta ƙara kuɗin lantarki a Najeriya

Spread the love

Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta amince da ƙara kuɗin wuta ga abokanan hulɗarsu da ke ajin Band A – masu samun wuta tsawon sa’a 20 a rana.

Mataimakin shugaban hukumar, Musuliu Oseni ya bayyana cewa a yanzu kwastamomin za su biya N225 kan kowane kilowatt inda a baya suke biyan N66.

A taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Laraba, Oseni ya ce abokan hulɗarsa da ke samun wuta tsawon sa’a 20 a rana sune kashi 15 cikin 100 na kwastamomin hukumar a Najeriya.

Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma sauke kwastamomin da ke ajin Band A zuwa Band B masu samun wuta ƙasa da sa’a 20 a rana saboda rashin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki na basu wutar da ta kamata.

Ya bayyana cewa ƙarin ba zai shafi kwastamomin da ke sauran matakan ba.

Tun bayan samun bayanai cewa hukumomi na iya ƙara kuɗin wuta ne, al’ummar Najeriya ke ta martani a shafukan sada zumunta inda wasu ke ganin matakin ya zo a lokacin da jama’a ke fama da tsadar rayuwa da kuma rashin tsayayyiyar wutar lantarki da ake fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *