Gwamnati za ta ƙara yawan mutanen da za ta bai wa tallafin kuɗi

Spread the love

Gwamnatin Najeriya na shirin sake fara bai wa talakawan kasar da kuma mafiya rauni miliyan 12 kuɗaɗen tallafi.

A halin yanzu, kusan mutane miliyan uku ne ke amfana da wadannan shirye-shiryen na tallafi, amma saboda tsadar rayuwa, gwamnati na sa ran karin iyalai miliyan 12 za su cancanci karɓan wadannan kudade.

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, ne ya sanar da wannan shirin yayin wani taron ma’aikata a Uyo, da ke jihar Akwa-Ibom.

Ministan ya ce manufar ita ce a bayar da tallafin kuɗi ga al’ummar da ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da domin magance buƙatunsu na gaggawa, ta yadda za a rage talauci.

Gwamnatin Binuwai Ta Ba Wa Makiyaya Wa’addin Ficewa Daga Jihar

Ba Gudu Ba Ja Da Baya Kan Zanga-Zangar Gama-Gari Da Za Mu Gudanar — NLC

Shawarar sanar da shugaba Tinubu kan shawarar kwamitin ɗin kafin a kammala rahoton karshe shi ne a sanar da shi abubuwan da ke faruwa.

Edun ya jaddada yin amfani da fasaha don tabbatar da biyan kuɗi mai inganci da gaskiya, da guje wa ayyukan hannu da jinkiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *