Gwamnatin jahar Edo ta dage ranar komawar daliban makarantun Sakarandire da Firamare sakamakon karin farashin kudin man fetur .
Gwamnatin jahar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar ilimi Ojo Akin-Longe, ya fitar a Benin ranar Asabar.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa, a ranar 9 ga watan satumba 2024, aka sanya a matsayin ranar komawar daliban, amma saboda karin farashin fetur din aka dage zuwa wani lokaci anan gaba.
Dage ci gaab da karatun ya shafi makarantun gwamnati da kuma masu zaman kansu a fadin jahar.
- Yar Najeriya ta lashe azurfa a gasar nakassu ta Paralympic
- Hon. Tajuddin Abbas Ya Samar Da Hadin Kai, Fahimtar Juna A Majalissar Wakilan Nigeria : Dr. Rufa’i Danmaje