Gwamnatin Enugu ta kashe kaji 30,000 a yayin rusau

Spread the love

An shiga halin fargaba a unguwar Nike da ke jihar Enugu a kudancin Najeriya, bayan gwamnati ta fara rusa gidajen mutane don gina wani sabon birni.

Mai gonar UD da ke unguwar ta Nike, Ngozi DeDe cikin hawaye ta bayyana cewa an kashe mata dabbobin da take kiwo da suka haɗa da kifi da kaji da darajarsu ta kai naira miliyan 30.

Mazauna unguwar da dama sun koka cewa gwamnati ba ta basu wata sanarwa ba kan rushe gidajen nasu, sai kawai a ranar Talata suka ga an fara rusau.

Ngozi ta shaida wa BBC cewa ” A ranar talata sai jami’an hukumon ma’aikatar Enugu suka fado mana, suka rusa gidan kaji na, kuma ba a bani wata sanarwar yin hakan ba kafin sannan.”

NPFL MD 23: Abia Warriors’ Daniel Ijeh voted SWAN Kano Pop Cola Man of the Match

Za mu tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abinci – NEMA

A cewarta a bara gwamnatin ta bayar da takarda, amma ita an gaya mata cewa bata cikin waɗanda abin zai shafa, sai gashi an zo an rushe mini gidan kaji.”

Ngozi Dede ta ce an kashe mata kaji 30,000 da kifi tarwaɗa 1,000 a gidan kaji uku da tare da lalata mata gidan ma’aikata biyu.

Yayin rusau da gwamnatin ta yi ya shafi kimanin gidaje 50.

Gwamnatin jihar ta Enugu ta sanya hannu a wata takarda na gina wani sabon birni a unguwar ta Nike.

Sai dai ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnatin ta Enugu bata kai ga mayar da martani ko amsa sakonnin da BBC ta tura mata game da wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *