Gwamnatin Jahar Kano Zata Fara Hukunta Ma Su Zubar Da Shara A Wuraren Da Aka Haramta.

Spread the love

Gwamnatin jihar kano ta bayyana shirin ta na daukar tsattsauran matakin doka a matsayin hanyar data rage mata wajen hana mutane zubar da shara a wuraren da aka haramta.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago , ne ya bayyana hakan lokacin daya jagoranci shugaban hukumar KAROTA,  Faisal Mahmud, yin rangadin wuraren da aka hana zubar da sharar.

A cewar Dan Zago gwamnati ba zata lamunci halin rashin kishi da kula muhallai da wasu suke nunawa ba ta hanyar zubar da shara barkatai a fadin jahar Kano, a dan haka ne hukumar sa ta hada hannu da hukumar KAROTA domin daukar mataki akan masu zubar da sharar a wuraren da aka haramta.

Da yake nasa jawabin, Shugaban hukumar KAROTA, Faisal Mahmud ,ya ce hukumar sa zata girke jami’anta a wuraren da gwamnati ta hana zubar da sharar domin daukar matakan da suka dace dan ganin an tsaftace jihar Kano.

Wuraren da gwamnati ta ce za’a fara da su wajen tursasa hana zubar da sharar sun hada da Kwari ‘Yan Hula, jikin katangar asibitin Kashi na Dala wato Orthopedic, sai gadar kasa ta kofar Ruwa da saman gadar da sauran gurare da hukumar bata amince a zubar da sharar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *