Gwamnatin Jahar Katsina Ta Rufe Gidajen Man Da Ake Zargin Suna Siyar Wa Yan Bindiga.

Spread the love

Gwamnatin jihar Katsina ta rufe Gidajen Mai 3 da ake zargin su da hannu wajen saida wa ‘Yanta’adda Man Fetur a jihar Katsina.

Kwamitin dake yaƙi da Ɓoye Hatsi da Hauhawar Farashin kayan Abinci da gwamnati jihar Katsina ta kafa a ƙarƙashin jagoranci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati jihar Katsina Hon. Jabiru Salisu Tsauri, ya kai wani samame gami da rufe wasu Gidajen Man 3 da suka haɗa da Mai Mammada, Mamasco, da kuma Ajasco da ake zargin suna saida wa ‘Yanta’adda Man Fetur a jihar.

Majiyar jaridar Idongari.ng, wato Katsina Post , ta bayyana  cewa, jagororin kwamitin sun kai samamen a ranar Litinin 15 ga watan Afrilu, 2024, a  babbar hanyar da ta Kewaye birnin Katsina, inda aka yi kacibus da gidajen man dake  hanyar Jibia tare da kama Mutane 10 da ake zargi.

Da yake jawabi ga Manema Labarai bayan rufe gidajen man, shugaban kwamitin Hon. Jabiru Salisu Tsauri, ya ce kwamitin yana da damar ya damƙe duk wa su ‘Yan kasuwa da suke saida wa ‘Yanta’adda Abinci ko kayan masarufi ko Fetur domin yin zirga-zirgar ta’addanci ga junansu.

Haka kuma, ya jaddada cewar, an ba kwamitin dokar duk wanda suka kama da laifin, suna da damar riƙe shi har tsawon Awa 48 a wajen su kamar yadda aka ba jami’an ‘Yan sanda dokar tsare mai laifi na adadin wannan lokacin kafin akai Mutum kotu.

Shugaban kwamitin ya ce, ba su fito yawon binciken ba sai da suka samu bayanan sirri game da gidajen man a kan zargin da ake mu su na siyar da man fetur ga ‘Yan bindiga a jihar Katsina, ya ce daga cikin bayanan sirrin da suka samu sun tabbatar da cewar gidajen man suna saida wa ‘Yan bindigar man fetur ne cikin dare da kuma lokacin Asuba.

Kazalika, ya roƙi al’ummar jihar da su ci gaba da ba kwamitin bayanan sirri domin ayyuka ci gaba jihar da kuma samun zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *