Gwamnatin Jahar Zamfara Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-Zirga

Spread the love

Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da takaita zirga-zirga daga misalin karfe 7:00pm na Yamma zuwa 6:00am na safe, akan iyakokin ta da makotan jahohi.

Kwamishinan yada labarai na jahar Zamfara Manir Haidara, ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau babban birnin jahar.
Jahohin da suke makotaka da jahar Zamfara, sun hada da Katsina da kuma Sokoto.

Haidara ya ce kwamitin tsaron jahar, ne ya dauki matakin bayan kammala wani taron gaggawa da aka gudanar .

wannan dai ba zai rasa nasaba da matsalar tsaro da jahar Zamfara ke fuskanta ba, da yawaitar yan ta’adda masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *