Gwamnatin jihar jigawa ta tabbatar da rahotannin da ke cewa ta bankaɗo ma’aikatan bogi sama da 6,000.
Gwamnatin ta ce ta gano hakan ne ta hanyar tantance ma’akatan jihar da aka gudanar,inda aka samu ma’aikata 50,800 daga cikin 57,236 da ake da su tunda farko,
Sagir Musa Ahmed Kwomishinan Watsa labarai da kula da bunkasa rayuwar matasa da wassannin motsa jiki da kuma raya al’adu na jihar Jigawa ya bayyanawa BBC cewa an fara tantancewar ne daga kan gwamnan jihar da manyan jami’an gwamnati, “Ta haka ne aka gano ma’aikatan na bogi.”
Gwamantin ta ce duk wata tana asarar kudin da suka kai sama da naira miliyan 300, wato sama da biliyan uku a shekara, “Wadanda za a iya karkatasu zuwa wani ɓangaren wajen yi wa al’umma aiki.”
Sagir Ahmed ya ce gwamnatin a dauki matakin ne domin tsabtace aikin gwamnati a jihar.