Gwamnatin jihar Enugu ta umarci coci-coci da masallatai su cire duk lasifikarsu ta waje

Spread the love

Gwamnatin jihar Enugu a Najeriya ta umarci dukkanin majami’u da masallatai a jihar su cire duk wata lasifika da suka sa a wajen gine-ginensu cikin kwana 90, sannan kuma su dauki matakan tabbatar da cewa hayaniya ko karar abubuwan da ake yi a cikin wuraren ibadar ba ta fitowa waje.

An dauki matakin ne a yau Alhamis, a lokacin wani taro tsakanin hukumomin da shugabannin Kiristoci da Musulmi a jihar, kan aiwatar da tsarin gwamnatin jihar na takaita hayaniya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar raya babban birnin jihar ta Enugu, Uche Anya, wanda ya bayar da umarnin ya ce hayaniya da kara sun zama babbar matsala ga jihar.

Shugaban ya nuna takaicin yadda ofishinsa ya samu koke sama da 1,000, daga masu gidaje a kusa da wasu coci-coci da masallatai da wuraren rawa ko shaye-shaye da makamantansu a kan kara ko hayaniya da ke damunsu

A shekarar da ta wuce, 2023, gwamnatin jihar, da ke kudu maso gabas, a wani mataki na sake tsarin raya biranenta, ta umarci dukkanin wuraren nishadi da sharholiya da shaye-shaye da kade-kade da sauran abubuwa na walwala da su takaita hayaniyar da ake yi a wuraren, a babban birnin jihar, musamman ma a unguwannin da gidajen jama’a suke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *