Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki nauyin nuna wasan Najeriya a wasu wurare

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ɗauki nauyin nuna wasan ƙarshe na Kofin Afirka na (Afcon) da Najeriya za ta fafata da ƙasar ivory Coast mai masaukin baƙin gasar a yau Lahadi da maraice.

Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Abdallah Yunus Abdallah ya wallafa a shafinsa na X ya ce za a nuna wasan a waɗansu wasu manyan makarantun jihar.

Yan Kasuwa a Kano Sun Koka Kan Kama Kayansu da Hukumar Kwastom Keyi

Shugabannin kananan hukumomi uku sun fice daga APC zuwa NNPP mai mulkin Kano

Wuraren da za a nuna wasan kyauta sun haɗar ta wuraren nuna wasanni na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da jami’ar jihar Kaduna, da Kwalejin fasaha ta KASU da Kwalejin ilimi na Gidan Waya da Kwalejin gwamnatin tarayya ta Zariya.

Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshen.

Najeriya na fatan lashe kofin na Afirka karo na huɗu a tarihi, idan ta yi nasara a kan Ivory Coast.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *