Gwamnatin jihar Oyo ta rufe coci saboda damun maƙwabta da hayaniya

Spread the love

Gwamnatin jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta rufe wata majami’a a rukunin gidaje na Golden Estate da ke unguwar Oluyole a babban birnin jihar, Ibadan saboda makwabta sun yi ƙorafi ana damunsu da ƙara a lokacin ibada a cocin.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Dotun Oyelade ya bayyana a wata sanarwa a yau Juma’a cewa an ɗauki matakin ne bayan yunƙuri da dama da ma’aikatar kula da muhalli ta yi na ƙoƙarin sasanta masu ƙorafin da kuma hukumar cocin ya ci tura.

An tsananta tsaro a wasu ƙananan hukumomin Kaduna saboda zaɓe

Mista Oyelade ya ce, ”saboda haka ne ya kasance gwamnatin jihar ba ta da wani zaɓi da ya wuce na ta rufe cocin domin gudun kada lamarin ya ƙazanta tsakanin mazauna unguwar da cocin.”

A baya mazauna unguwar sun taɓa rufe ƙofar shiga rukunin gidajen domin hana masu ibada a cocin shiga.

Gwamnatin jihar ta yi gargaɗin ɗaukar matakin shari’a a kan majami’u da masallatai da gidajen shaƙatawa da ma’aikatu da kamfanoni da kasuwanni kan buɗe lasifika ko hayaniya da za ta damu jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *