Gwamnatin Kaduna ta bai wa masu zanga-zangar da aka saki kyautar wayoyi da kuɗi

Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bai wa masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka saki kyautar manyan wayoyi da kuɗi kimanin naira 100,000.

Gwamnan ya kuma alƙawarta bai wa mutum 39 ‘yan jihar da aka saka -horo domin sake musu tunani, tare da ba su jari, idan sun kammala samun horon.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdulkadir Meyere ne ya bayyana haka, kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.

Ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya bayar da umarnin da ya karɓi takardun matasan da suka kammala karatu a cikinsu.

“Gwamna ya alƙawarta cewa za a bayar da jari ga wasunsu domin su fara sana’a, yayin da za a koya wasu sana’o’in wasu kuma gwamnati za ta ɗauke su aiki,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *