Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya musanta raɗe-raɗin biyan ’yan bindiga kuɗi domin sulhu don su ajiye makamai.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu ko tattauna da mahara.
Wannan dai ka zuwa ne, bayan da wasu rahotanni suka nuna cewar gwamnatin jihar na biyan mahara kuɗi domin su ajiye makamansu don yin sulhu.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels, gwamnan ya ce, “Ba mu ba su ko sisi ba. Yawancinsu sun gaji, kuma mun tambaye su dalilin da ya sa suke ci gaba da kai hare-hare da garkuwa da mutane.”
A ranar Alhamis, jihar ta karɓi rukunin farko na ‘yan bindigar da suka tuba a Birnin-Gwari tare da sake buɗe kasuwar shanu da aka rufe sama da shekaru 10 saboda matsalar tsaro.
Gwamna Sani, ya bayyana cewa ya ɗauki watanni shida yana yin haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na tarayya, don cimma ganin an yi sulhun.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen karɓe makamai daga hannun waɗanda suka tuba.
- N-power : Taurin Bashi Ya Sanya Matasa Za Su Gudanar Da Zanga-zangar Kwanaki 5.
- Saudiyya na dab da samun damar karɓar baƙuncin gasar cin Kofin Duniya na 2034