Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana fita

Spread the love

Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita da ta sanya sakamakon tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar matsin rayuwa, inda yanzu jama’a za su iya fita daga karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma.

A sanarwar da kwamishinan kula da harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce bayan nazarin yanayi da majalisar tsaro ta jihar ta yi a yanzu ta rage lokacin dokar ta sa’a 24, wadda aka sanya ranar Litinin 4 ga watan Agusta, 2024.

Da wannan sassauci sanarwar ta ce daga yanzu jama’a za su ci gaba da kasancewa a gida daga karfe 6 na yamma har sai karfe takwas na safe sannan su fito su ci gaba da gudanar da harkokinsu.

Kwamishinan ya jadda cewa jami’an tsaro za su ci gaba da tabbatar da ganin jama’a sun kiyaye tare da bin umarnin da aka bayar na bin dokar, da tabbatar da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *