Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce za ta dasa bishiyoyi 20,000 a 2024 a fadin jihar.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar Abubakar Buba ne ya bayyana hakan yayin wani taron kwana ɗaya kan manufofin sauyin yanayi a jihar, taren da haɗin gwiwar kungiyar Save the Children.
Ya ce shirin wani yunkurin ne na rage tasirin sauyin yanayi da ake fama da shi a jihar da ma ƙasa baki daya.
- Hukumar Karota Ta Cafke Motoci Makare Da Giya A Kano
- Gwamnan Kano zai cika wa maniyyatan jihar naira dubu 500
Da take nasa jawabin babbar sakatariyar ma’aikatar Linda Yakubu wadda ta wakilci kwamishinan ta ce matuƙar ana son ɗorewar jihar Kaduna do dole a yi wani abu game da lamarin sauyin yanayi.
“Sauyin yanayi gaskiya ne kuma mun fara ganin tasirinsa a jiharmu. Za a gabatar da sabbin manufofi da za a rage tasirinsa a jihar.”