Gwamnatin Kano ta bankado haramtattun gine-gine 68

Spread the love

Hukumar Tsara Birni ta Kano KNUPDA ta sanar da bankaɗo wasu haramtattun rukunin gine-gine 68 da aka yanka filayensu ba bisa ka’ida ba.

Manajan Daraktan KNUPDA, Arch. Ibrahim Yakub Adamu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a wannan Larabar.

Najeriya ta sanya harajin dole ga kamfanonin da ke ɗaukar ma’aikata daga ƙetare

A rufe duka layukan da ba haɗa da NIN ba – NCC

Adamu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin da KNUPDA ta kafa wanda zai binciki yadda aka gididdiba filayen tare da sayar da su a jihar ba tare da samun izinin gwamnati ba.

Adamu wanda ya bayyana matuƙar damuwa kan lamarin da ke wargatsa tsarin gine-gine, ya yi gargadin cewa gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace a kan masu kunnen kashi da karya doka.

Jami’ar hulda da jama’a ta Hukumar KNUPDA, Bahijja Mallam Kabara, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana cewa, Arch Adamu ya ce ɗaukar wannan matakin ya yi daidai da manufar gwamnatin Kano ta Abba Kabir Yusuf na ganin Kano ta shiga sahun jihohi a kasar nan a fannin tsara birane.

Aminiya ta ruwaito cewa, kwamitin da KNUPDA ta ƙaddamar zai kasance karkashin jagorancin jami’in tsara birane, Junaid Abdullahi, yayin da sauran mambobin kwamitin sun haɗa da dukkan daraktoci da wakilan kamfanoni masu zaman kansu a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *