Gwamnatin jihar Kano ta dage ranar da za a koma makarantun firamare da na sakandire domin fara karatun shekarar 2024/2025.
Wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu ta ruwaito kwamishinan ilimi Alhaji Umar Haruna Doguwa yana bayyana cewa an yanke shawarar dage ranar da za a koma makarantar ne saboda wasu dalilai na gaba gaggawa.
Umar Doguwa ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba ma’aikatar ilimi ta jihar kano za ta sanar da wata rana da za a komawa makarantun.
- An Gurfanar Da Wani Mutum Da Kunshin Takaddun Tuhuma 8 A Kano.
- Gwamnatin Edo Ta Dage Ranar Komawa Makaranta Saboda Karin Man Fetur
“Ina so in sanar da dalibai da iyayensu cewa sanarwar da aka bayar tun farko na komawa makarantu a ranakun 8 da 9 ga Satumba, 2024, yanzu an dage ta, saboda wasu dalilai na gaggawa da za su taimaka wajen inganta yanayin koyo da koyar da yaranmu. za a sanar da wata ranar nan gaba kadan, “in ji kwamishinan.
We are waiting