Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Haska Fina-finan Hausa 22

Spread the love

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da haska shirin Labarina, Dadin Kowa da wasu ƙarin fina-finan Hausa guda 20 a kafafen Internet ko gidajen talabijin.

Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne a ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara dora masana’antar Kannywood a kan saiti.

A cewar wata sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar da daren Lahadi, fina-finan da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Labarina, Dadin Kowa, Manyan Mata, Garwashi, Jamilun Jidda da kuma Gidan Sarauta.

Sanarwar ta ce umarnin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, bayan wani zamanta da kuma tattaunawar da ta gudanar.

 

Jerin fina-finan da aka dakatar

Sanarwar ta bayyana jerin fina-finan da dakatarwar kamar haka:

  1. Ɗakin Amarya
  2. Mashahuri
  3. Wasiyya
  4. Tawakkaltu
  5. Mijina
  6. Wani Zamani
  7. Mallaka
  8. Kuɗin Ruwa
  9. Boka Ko Malam
  10. Wa Ya San Gobe
  11. Rana Dubu
  12. Manyan Mata
  13. Fatake
  14. Gwarwashi
  15. Jamilun Jiddan
  16. Shahadar Nabila
  17. Daɗin Kowa
  18. Tabarma
  19. Kishiyata da kuma
  20. Rigar Aro.

Hukumar ta ce ta ɗauki gagarumin matakin ne domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne fim gabanta a tantance shi kafin a sake shi.

Sanarwar ta kuma ce doka ce ta ba Hukumar damar tace duk wani fim tare da lura da ayyukan ’yan masana’antar Kannywood matukar suna da rajista da hukumar a ko ina suke.

“A saboda haka, ana shawartar masu ɗaukar nauyin waɗannan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen talabijin ko kafar internet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *