Gwamnatin Kano ta kaddamar da feshin maganin sauro a kananan hukumomi 8 na birnin jahar.

Spread the love

Shugaban hukumar kwashe shara na jahar Kano, Ambasada Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ya bukaci al’ummar kananan hukumomi 8 na kwaryar birnin Kano da su ba wa jami’ansu hadin kai akoda yaushe.

Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ya bayyana hakan a lokacin da yaje kaddamar da shirin feshin maganin Sauro da aka gudanar a Unguwar Kwanar Diso dake birnin Kano.

Shugaban hukumar ya ce daman ana yin feshin maganin a baya, amma sakamakon zuwan sanyi sai sauron ya ragu, sai dai a wannan lokaci ne ya dawo tare da kudirin ganin an kaishi kasa saboda magance cutar cizon sauro.

Ya kara da cewa, hukumar ta Remasab, an dawo da ita ne a ranar 4 ga watan Yuli 2023 ,domin ci gaba da tsaftace gari , wadda abaya wasu dalilai suka sanya aka rushe ta saboda rashin kishi.

Ya ce hukumar aikinta shi ne kwashe shara, tsaftace muhalli da yin feshin don magance sauro da sauran kwaruka.

” wannan hukuma idan za ku iya tuna wa a shekarar 2011 tsohon gwamnan jahar Kano Sanata Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso , ya bata muhimmaci wajen fashin maganin sauro da kwashe shara , dukkan ma’aikatan hukumar shaida ne” Ahmad Zago”.

Ya kara da cewa, gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf , ya zabi kyautata rayuwar al’ummar jahar wajen samar da abubuwan rayuwa da kare dukiyar su da lafiyar su.

Hakanne ya sanya hukumar kwashe sharar dake karkashin ma’aikatar muhalli ta jahar Kano , ta ga dacewar kyautata wa al’umma bisa umarnin gwamnatin jahar Kano.

Ya ce feshin za a ci gaba da yi, a kananan hukumomin 8 na birnin Kano saboda kwari da Macizai musamman a makarantun kwana .

” Mai girma gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf , kowa ya sani zuwa ya yi ya taimaki al’ummar Kano musamman wajen aikace-aikace”.

Haruna Zago ya ce nan da ranar litinin za a biya dukkan ma’aikatan wucin gadi na hukumar kudaden su.

Mai unguwar Diso Ahmad Bello Diso , ya godewa tawagar hukumar kwashe sharar bisa yadda suka kaddamar da feshin maganin sauron a unguwarsa, inda ya bukaci al’umma su ci gaba da ba su hadin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *