Gwamnatin Kano ta kafa kotun hukunta yan kwaya da yan fashin Waya.

Spread the love

Kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi da fashi waya a Jihar Kano ya kafa kotun tafi da gidan ka domin gaggauta hukunta wadanda ake zargi da aikata laifi.

Shugaban kwamitin, Birgediya Gambo Mai’Adua (mai ritaya) ya gargadi ma su, yi cewa su daina ko su gamu da fushin hukuma, domin gwamnatin jihar ba za ta lamnuci ayyukansu ba.

“Kwamitin yana da kotun tafi da gidanka kuma yana da niyyar gyara dabi’ un wadanda suka daina da kuma mayar da su cikin al’umma,”

Gambo Mai’Adua ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan yakin da kwamitin ke yi na yaki da shan miyagun kwayoyi da fashin wayoyin salula a jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, akwai abin damuwa a cikin wani rahoto na baya-bayan nan da ke nuna a duk mutum shida a jihar, daya na shan miyagun kwayoyi, don haka gwamnatin jihar ta kaddamar da yaki da duk masu hannu a cikin lamarin.

Ya bayyana cewa kwamitin yana aiki tare da sauran hukumomin da ke aiki kan shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran laifukan masu alaka da su, don ganin an shawo kan yawan shan miyagun kwayoyi a Jihar Kano.

Ya kara da cewa, yaki da wadannan matsalolin hakki ne na kowa da kowa, inda ya ce Magance wannan barazanar tun yanzu shi ne abu mafi alheri gare mu da al’ummarmu”.

Jami’in kuma yi nuni da cewa, kwamitin zai mayar da hankali wajen farfadowa, sauya tunanin, da kuma dawo da wadanda abin ya shafa cikin al’umma idan sun daina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *