Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta, a unguwar Rijiyar Zaki Kano, ta sanya ranar 19 ga watan Nuwamban 2024, don bayyana matsayarta kan tuhumar da ake yi wa matashinnan mai suna Shafi’u Abubakar, kan zargin kone wasu masallata a garin Gadan dake karamar hukumar Gezawa ta jahar.
Tuni dai bangaren ma su kara suka kammala gabatar da shaidunsu guda 7 , a zaman kotun na ranar Talata 12 ga watan Nuwamban 2024.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa a zaman da ya gabata, ma su gabatar da karar sun gabatar da wani jami’in dan sanda mai suna ASP Abdullahi Sajau, da ya jagoranci gudanar da binciken da ake yi wa Shafi’u Abubakar, bayan jami’an yan sandan Gezawa sun mika shi, babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan Kano.
ASP Abdullahi Sajau, ya shaida wa kotu cewa ‘’ sun ziyarci asibitin Murtala Muhammed, inda suka tarar da da mutane 25 wadanda suka gamu da iftila’in , kuma ana zargin shafi’u ne ya kona su bayan ya siyo man fetur na naira dubu bakwai ‘’.
- Gwamna Abba Kabir da manyan mutane za su halarci auren ’yar Sanata Kwankwaso a Kano
- Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato
Ana tuhumarsa da laifukan kisan kai ta hnayar kunna wuta da yunkurin kisan kai ta hanyar zuba man fetur da kuma tayar da hankalin al’ummar garin Garin.
Lauyan gwamnatin jahar Kano, Barista Salisu Muhd Tahir, ya bayyana cewa sun kammala gabatar da shaidunsu kan wanda ake zargin.
Lauyar da ke kare wanda ake tuhuma Barista Hasiya Mohd Imam, ta ce basa yin suka kan shaidun da da masu gabatar da kara suka gabatar, amma a zama na gaba wanda ake zargin zai fara kare kansa.
Alkalin kotun mai shari’a Halhalatul kuza’I Zakariya, ya sanya ranar 19 ga watan Nuwamban 2024, don ci gaban shari’ar