Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Da Ake Zargi Da Belin Danwawu

Spread the love

Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin binciken zargin kwamishinan sufurin jihar Ibrahim Namadi da hannu a belin mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar ya miƙa wa gwamnati rahotonsa.

A yau Litinin ne kwamitin ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton binciken nasa ga sakataren gwamnatin jihar.

Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, to sai dai matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai fayyace abin da kwamitin ya gano a binciken nasa.

A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin, bayan da aka zargi Namadi da ƙarbar belin Danwawu, mutumin da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi.

Batun ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na kwamishina ya karɓi belin mutumin da ake zargi da taimakawa wajen assasa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.

Lamarin da ya sa wasu ke ta kiraye-kirayen sauke shi daga muƙaminsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *