Gwamnatin Jahar Kano ta bayyana cewa ba za ta kyale Direbobi suna ci gaba da Gudun Wuce Sa’a, suna kashe Mutane ba.
Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ne ya furta, hakan a ya yin ziyarar ta’aziyar da ya kai Garin Imawa dake karamar hukumar Kura, bayan da wata karamar mota ta Yi kan mutane da dama lokacin da suke sallar juma’a.
Rahotanni na cewa mutane Uku ne Suka rasu , sannan wasu hudu kuma suna kwance a asibiti.
Hakanne ya Sanya al’ummar yankin rufe babbar hanyar Kano zuwa Zaria, tare da bankawa motar Wuta har ta Kone kurmus.

- Yan Sanda Sun Kama Ma Su Garkuwa Da Mutane 11 A Kaduna
- Kotu Ta Dakatar Da KANSIEC Karbar N10m Da N5m Kudin Tsayawa Takarar Chairman Da Kansila
Tuni dai gwamnan jahar Kano Engr.Abba Kabir Yusuf, ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su, da kuma Yi wa wadanda suka jikkata addu’ar Samun lafiya.
Haka zalika Gwamnan, ya ziyarci asibitin da aka kwantar da wadanda suka jikkata, harma da daukar nauyin kula da lafiyarsu.
A cewar Abba Kabir Yusuf , al’ummar yankin su dauki lamarin a matsayin mukaddari, domin kowanne Mai rai ya dandani Mutuwa, Inda ya tabbatar mu su da cewar Gwamnatin Kanon zata Yi mu su Gadar Sama don tsallakawa.
Ya kuma ja hankali Direbobi musammana su yin gudu Wuce Sa’a, da su dinga yin taka tsantsan, a lokacin tuki don duk Wanda aka kama za a Hukunta shi.
Wakilin idongari.ng, dake yankin ya ruwaito cewa tunda yammacin ranar juma’a al’amura suka koma daidai Inda aka bude hanyar don matafiya su samu damar Wuce wa .