Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahoton da ake ya madidi da shi, kan siyan wasu Dabbobi da za a raba wa jama’a , wai an siye kowacce Akuya kan kudi naira dubu 350 inda gwamnatin ta ce ba gaskiya ba ne.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aike da manema labarai ayau Alhamis a birnin Kano.
Waiya ya ce an siyi Akuyoyi guda dubu 7158 kan kudi naira miliyan 451, inda za a raba wa mutane dubu 2386, sai Raguna guda 1975 kan kudi naira miliyan 351 da dudu 750 da za raba su ga mutane 987.
Haka zalika an siyi Shanu guda 1400 kan kudi naira biliyan 1 da miliyan 120 wadanda za a raba wa mutane 700, sai kuma kudin ciyarwa da magani da sauran hidinhimu da aka ware na naira miliyan 427 da dubu 958.
Kwamishinan ya kara da cewa jimullar kudin da aka ware sune naira Biliyan 2 da naira miliyan 350 sabanin abinda ake yada wa kan cewar kowacce akuya an siye ta kan naira dubu 350.
- Sojoji sun Kashe Mataimakin Bello Turji
- Gwamnatin Kano ta haɗa gwiwa da Media Trust kan inganta harkokin yaɗa labarai
‘’’wannan shi ne abunda aka ware ko aka yi da su wato naira miliyan dubu 2 da naira miliyan 350 sabanin abinda mutane suke ta yamadidi da shi’’ Waiya.
Sai dai waiya ya yi zargin cewa an yada labarin da gangan dan a bata gwamnati har ya shawarci manema labarai su dinga bincike kafin su yada wani abu don kaucewa yada fitina a tsakanin al’umma.
‘’Wannan ba daidai ba ne yakamata al’umma su dinga jin tsoron Allah kan abubuwan da suke yi kuma su fahimci cewa ya madidi da abinda yake na zance na karya ba daidai ba ne’’ Waiya’’.
A karshe Waiya ya ce duk wanda ya duba jawabin gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dukkan adadin kudaden da aka yi daki-daki.