Gwamnatin jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, ta sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma.
Wannan dai na daga cikin abubuwan da aka tattauna ya yin taron majalisar koli ta harkokin tsaron jihar da aka yi a yau Talata karkashin jagorancin gwamnan jihar.
A gefe guda kuma an bude manyan kasuwannin jihar na wucin gadi, inda aka yi hada-hada daga safe zuwa karfe daya na rana.
An sanya dokar hana fitar ne, a ranar Alhamis din ta wuce, wato ranar da aka fara zanga-zangar matsin rayuwa a fadin kasar, sakamakon rikidewar da zanga-zangar ta yi ta koma tarzoma.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ne ya sanar da saka dokar ce ta tsawon awa 24 bayan wasu ɓata-gari sun farfasa tare da wawashe kayayyaki a shagunan ‘yan kasuwa da gine-ginen gwamnati yayin zanga-zangar.
Ƙarin abin da ya ta’azzara al’amuran na Kano shi ne yadda maƙwabtan jihohi na Kaduna da Katsina da Jigawa suka saka dokar hana fitar, duka saboda tarzomar ɓata-garin.
Daga bisani an sassauta dokar, inda aka mayar da fita harkoki daga karfe 8 na safe zuwa biyu na rana.
Jihar Kano na cikin wuraren da zanga-zangar ta fi rikiɗewa zuwa tashin hankali, inda rahotonni ke cewa an kashe mutane da dama.
Sai dai har kawo yanzu babu wasu alƙaluma daga gwamnati ko ‘yan sanda na yawan waɗanda suka mutu.
A ranar Litinin ma – rana ta biyar – masu zanga-zangar sun fita wasu titunan birnin ɗauke da tutocin Rasha, yayin da rundunar ‘yan sandan jihar ta ce tana ci gaba da bin sawun kayayyakin da aka sace.