Gwamnatin Kano Ta Soke Aiyukan Kungiyoyi Ma Su Alaka Da Auren Jinsi A Jahar.

Spread the love

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta bayyana matsayarta da kuma ta gwamnatin jahar, kan danbarwar da ta kunno kai na sanya hannu kan wata yarjejeniya ta SAMOA tsakanin kashen turai da kuma nigeria.
Hukumar ta ce gwamnatin jahar ba ta gamsu b, kuma ba ta yadda da duk wani abu da zai ci karo da addinin musulinci ko kuma dokar da aka kaddamar ta addinin musulinci a jahar Kano.
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jahar Kano Asheik Dr. Aminu Ibrahim Daura, ne ya bayyana hakan ga jaridar idongari.ng, a ranar Litinin a shelkwatar hukumar da ke unguwar Sharada Kano.
Asheik Daura, ya ce duk wata yarjejeniya ta ke a fili ko a boye wadda ta ci karo da dokar da aka kafa ta addinin musilinci a jahar Kano, da kuma dokar musulinci harma da dokar kasa ta shekarar 2013 wadda ta haramta auren jinsi da mu’amula da kafa kungiyoyi da goyon baya da duk wata ma’amula da ta shafi wannan lamari ba za su amince da ita ba.

Shekarar 2013 tsohon shugaban kasa Godluck Jonathan, ya sanya wa hannu wadda ta yi cikakken bayani kan haramcin goyon bayan auren jinsi a fadin Nigeria.
” saboda haka gwamnatin jahar Kano ba ta amince da hakan ba” cewar Daurawa”
Kwamandan hukumar Hisbar ya kara da cewa daman hukumar ta da dade ta shiga lungu da sako wajen wayar da kan mutane, don su kauce wa shiga irin wadannan kungiyoyi na auren jinsi.

Ya kara da cewa abaya sun sun kama irin wadannan mutane har suka gurfanar da su agaban kotuna daban-daban kuma a yanzu haka suna ci gaba da yaki da yan Daudu.

Hukumar Hisbar ta ce wasu kungiyoyi da yawa sun shigo jahar Kano, inda suke gudanar da aiyukansu daban-daban, ya yin da wasu ke bayar da tallafi wasu kuma bayar da aikin yi, inda hukumar ta zargi su da alaka da waccan akidar.

Sai dai hukumar ta ce yanzu ta fara bibiyar kungiyoyin domin taka mu su burki, kum duk kungiyar da aka samu ta shigo jahar Kano da kowanne irin suna gwamnati da kuma Hukumar Hisbah ba za su amince da aiyukansu ba.

” Saboda haka duk wata kungiya da ta shigo jahar Kano da irin wannan an soke aikin ta ” Sheik Ibrahim Daurawa”.
Sheik Aminu Daurawa , ya musanta wani faifen bidiyo da ake zargin wani jami’in bayar da taimakon gaggawa na hukumar Hisba, Idris Ahmed Gama, ya fito ya yi wasu jawabai har ya alakanta kansa da hukumar Hisbah wanda jama’a suka so jin gaskiyar lamarin.

Hukumar ta ce ba gaskiya ba ne abunda ya fada , domin ita Hisbah yaki ta ke yi duk wani abu da ya saba da addini.

”Ba mu yadda a dukkanin ofisoshin hukumar Hisbah na kananan hukumomi 44 , su yi mu’amula da duk wata kungiya da sunan bayar da taimako, duk jami’in da mu ka samu za mu dauki mataki akansa.
Daura ya ce za su dauki mataki na shari’a kan matashin da ake zargi da yin amfani da sunan Hisbah ba tare da sanin hukumar ba.

Jaridar idongar.ng, ta zanta da wanda ake zargin, Idris Ahmed Gama, inda ya shaida wa jaridar cewa, an gayyace shi wani taro ne shekaru biyu da suka gabata kuma bai san ma’anar LGBTQ ba, kuma sun gayyace shi a matsayinsa jami’in hukumar hisbah.
Wannan lamari dai ana ci gaba da tattauna wa a wurare daban-daban, inda yan Nigeria ke nuna rashin amincewarsu da auren jinsi, duk da cewar gwamnatin kasar ta musanta labarin da ake yada wa na cewar ta sanya hannu a yarjejeniyar da aka kulla da kasashen turawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *