Gwamnatin jahar Kano, ta Yi kira ga jami’an tsaro, musamman wadanda suka zama limamai, su ci gaba da yada karatuttuka ga jama’a domin zai kara mu su nutsuniya har su gane cewa jami’an hukumomin tsaron ma su tsoron Allah ne.
Kwamishinan ma’aikatar addinai na jahar Kano, Ahmed Tijjani Auwal, ne ya bayyana hakan, a wajen bitar Yini biyu da Rundunar Yan Sandan Kano, ta Shiryawa limamai da Ladanan hukumomin tsaron kasarnan.
Ahmed Tijjani ya ce, tabbas shirya wannan bitar , abin farin ciki ne kuma yakamata jami’an tsaron sun gane yadda addinin musulinci ya tsara al’amura musamman abinda ya shafe su na tsaro Wanda Ake yin komai a cikin hikima da adalci don Samar da tsaro a wannan Jahar.
” A irin wannan zama , zama ne na Allah , zama ne na addini Wanda ana Samun nutsuwa a ciki kuma Malamai sun kawo , Ayoyi Alkur’ani da Hadisai Wanda da gaske sun gamsar” cewar , Ahmed Tijjani Auwal”.
- Rudunar Yan Sandan Kano Ta Shiryawa Limamai Da Ladanan Hukumomin Tsaro Bitar Hanyoyin Isar Da Sako Da Yadda Ake Kiran Sallah Da Kura-kuran Da Ake Samu .
- Kungiyar POWA Ta Kammala Ziyarar Ganawa Da Matan Yan Sanda Da Iyalansu A Kano.
Ya kara da yin kira ga hukumar Yan Sandan ta ci gaba da shirya irin bitar harma da yadda su kansu Yan Sandan za a nuna musu yadda addini ya fadi kan tafiyar da aiyukan su.
A karshe ya ce Gwamnatin jahar Kano , a shirye ta ke , duk lokacin da suke da bukata za ta hada Kai da su kan irin wadannan taruka.
Taron bitar an Shirya ta ne don kara dankon zumunci Tsakanin su da sauran hukumomin tsaro, don tunatar da juna kan abinda ya shafi addinin musulinci musamman wajen isar da sako ga al’umma cikin hikima.