Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, za ta fara gurfanar da duk masu kin biyan kudaden haraji a shekarar 2025, a wani bangare na sauye-sauyen da ta ke yi a harkokin haraji.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 daga jihar Kaduna.
A cewar sanarwar, Shugaban Hukumar tattara kudaden haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dr. Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi ga Gwamnan Jihar a wani bangara na bita da gwamnatin jihar kano ta shiryawa manyan jami’anta.
Dr. Zaid Abubakar ya fayyace cewa za ai hakan ne ba wai don kara haraji ba, illa dai don inganta ayyukan tattara kudaden haraji da kuma tabbatar da bin ka’idojin haraji.
- Rundunonin sojin Najeriya sun yi wa manyan hafsoshi ƙarin girma
- An saki Yahaya Bello bayan cika sharuɗan beli
Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta yi hasashen samun kudaden haraji sama da naira biliyan ashirin a kowanne zango na shekarar 2025.
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf a kwanakin baya ya sauke tsohon shugaban hukumar tara kudaden haraji ta jihar tare da nada sabo, wanda hakan ya taimaka wajen kara inganta ayyukan hukumar a Zango na uku da na hudu na shekarar 2024.
Don tabbatar da gyare-gyaren ta fuskar tattara kudaden haraji, Gwamna zai kaddamar da wani sabon tsari na karbar haraji.