A Najeriya, yayin da wasu jihohi ke rige-rigen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, gwamnatin jihar Kano ma ta sanar da aniyar yin hakan.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayyana matakin shirya zaben ne jim kaɗan bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsu ta NNPP.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoton gwamnatin ba ta saka ranar gudanar da zaɓen ba.
Akwai jihohin Najeriya sama da 10 yanzu haka da babu zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomi, kuma a mafi yawan lokaci ana nuna shakku kan sahihancin zaɓen da hukumomin zabe na jihohi ke shiryawa.
Matakin dai na zuwa ne bayan hukuncin da kotun ƙolin ƙasar da ta yanke na amincewa da bai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin gashin kansu game da harkokin kuɗi.