Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai kaddamar da shirin raba kayan makaranta (Uniform) ga daliban Firamare yan aji 1 a fadin jihar a ranar Litinin 13 ga watan Janairu, 2025 a wani mataki da gwamnatin ta dauka domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar.
Kimanin dalibai sama da 789,000 maza da mata a makarantun gwamnati 7,092 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar ne ake sa ran za su karbi kayan Masarautar (Uniform)r a karkashin shirin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada Labarai na Kano Com. Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma ya aikewa da manema labarai a lahadi.
- NLO Appoints Muzammil Yola as Northwest Media Representatives
- Lakurawa Sun Kashe Ma’aikatan Kamfanin Airtel 3 A Jihar Kebbi
Gwamnatin Kano ta damu da sha’anin ilimi ne domin shi kadai ne zaka baiwa yara su inganta rayuwarsu da ta al’umma idan sun girma.
Taron kaddamar da ba da kayan Masarautar (Uniform) da zai gudana ne da karfe 1:00 na rana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf da kan sa zai kaddamar da shirin.
KADAURA24