Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na karfafa hadin gwiwa da kafafen yada labarai na intanet domin inganta yada bayanai ga al’umma.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka yayin taron tattaunawa da kungiyar kafafen yada labarai na intanet a Kano.
A yayin taron, Waiya ya jaddada muhimmancin kafafen yada labarai na intanet wajen isar da labarai cikin gaggawa ga al’ummar duniya. Ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa gwamnatin Kano a shirye take ta yi aiki tare da su domin isar da manufofi da shirye-shiryenta ga jama’a yadda ya kamata.
“Ku manyan abokan huldar gwamnati ne a fannin yada labarai, kuma rawar da kuke takawa ba ta da misali. Gwamnati za ta tabbatar da cewa kuna cikin shirye-shiryenta, ciki har da horarwa da sauran matakan bunkasa kwarewa don inganta aikin jarida,” in ji Waiya.
- CP Bakori Zai Maye Gurbin AIG Dogo A Matsayin Sabon Kwamishinan Yan Sandan Kano
- Bradford College Kano Enrolls Students in Tubless Innovation and Skills Centre for Photography and Content Creation Class.
Kwamishinan ya kuma bukaci ‘yan jarida su kiyaye ka’idojin aikin jarida, su mutunta hakkin kowane dan kasa, tare da yada sahihan labarai. Haka kuma, ya bukaci hadin kai tsakanin ‘yan kungiyar domin karfafa tasirinsu a fannin watsa bayanai ga jama’a.
A martaninsu, wakilan kungiyar sun jinjinawa Kwamishinan bisa yadda ya fahimci muhimmancin kafafen yada labarai na intanet.
Sai dai sun bukaci goyon bayan gwamnati, musamman a fannin kulla yarjejeniyoyi da su don tabbatar da ci gaban ayyukansu, tare da samar da horo ga sabbin ‘yan jarida da wadanda ke aiki a halin yanzu.