Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kirkiri wani tsari na musamman da Gwamnatin za ta rinka tattaunawa da al’umma kai tsaye dan jin matsalolin su tare da karbar shawarwari daga garesu.
Kwamishinan yada labarai Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kwamatin da gwamnan Kano ya kafa dan bincikar musabbabin rikice rikicen da aka samu lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan August shekarar da ta gabata ta 2024 a nan Kano.
Waiya ya kuma ce kowanne kwamishina da shugabannin ma’aikatu za su kasance a wajen taron tattaunawar danjin shawarwari da kuma koken da mutane ke dasu a ma’aikatun su.
- EFCC ta kama jami’an Gwamnatin Katsina kan sace tallafin N1.3b
- An Gurfanar da Daya Daga Cikin Wadanda Ake Zargi Da Kashe Dan Sanda A Kano.
Ya kuma ce hakan zai sa gwamnati ta san irin matsalolin dake damun al’umma kai tsaye.
Da yake jawabi shugaban kwamatin Justice Lawan Wada Muhammad mai Ritaya, da Farfesa Muhammad M Barodo yai magana a madadinsa cewa ya yi sun zo gun kwamishinan ne domin ta yashi murna kan mukamin da aka bashi.
Ya kuma ce idan har akai amfani da kudurorin da kwamishinan yazo da shi za a samu ci gaba ta fannini da dama a j
jihar Kano.